Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello
Mene ne matsayin auren mutu'a?
Auren Mutu'a, muhawarar kenan da ake tafkawa a arewacin Najeriya, kan halasci ko rashin halascinsa.
Abin ya faro ne da bidiyon limamin Babban Masallacin Ƙasa a Najeriya, Farfesa Ibrahim Maƙari yana bayani kan wata tambaya daga ɗalibansa da ke zaune a ƙasashen waje.
'Biyan bashi ne ke laƙume kuɗin Najeriya da aka tara bayan janye tallafi'
Ministan kuɗin Najeriya ya ce kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur da kuma gyaran tsarin kuɗaɗen ƙasashen waje sun fi karkata wajen biyan bashin gwamnati da kuma ɗawainiyar gudanar da gwamnati da ya ya ƙaru.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi a ƙasar ke ƙoƙarin kare sauye-sauyen tattalin arzikin da ake zargin sun ƙara tsananta rayuwar al'umma.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da waɗannan sauye-sauye a shekarar 2023, lamarin da ya samu goyon bayan masu zuba jari da cibiyoyin ba da lamuni na duniya.
Sai dai kuma sauye-sauyen sun haifar da tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ga miliyoyin ƴan Najeriya, abin da ya sa ake tambayoyi kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka ce an tanada bayan cire tallafin.
Da yake jawabi a taron African Emerging Markets Forum da aka gudanar a Abuja, Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce kafin cire tallafin, tallafin man fetur da abin da ya bayyana da wani na tallafin kuɗaɗen waje sun kasance suna cin kusan kashi biyar cikin ɗari na kuɗaɗen da ake samu a cikin ƙasar.
Oyedele ya ce wani ɓangare na kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin na tafiya ne wajen biyan bashin gwamnati, saboda kuɗin ruwa na lamuni ya ƙaru daga kusan kashi 8% zuwa har kashi 24% bayan aiwatar da sauye-sauyen.
Ya kuma ce albashin ma'aikatan gwamnati ya kusan ninka sau biyu, bayan da gwamnati ta ƙara mafi ƙarancin albashi daga baya zuwa naira 70,000 a wata.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙara kashe kuɗi kan shirin ba da rancen ilimi, wanda ke biyan kuɗin makaranta tare da ba ɗalibai fiye da miliyan 1.5 tallafin kuɗin rayuwa na wata-wata.
Oyedele ya yi watsi da rahoton Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) wanda ya ce miliyoyin 'yan Najeriya na ci gaba da rayuwa cikin talauci duk da sauye-sauyen tattalin arzikin. Ya ce raguwar ƙarfin sayen kuɗin jama'a na ɗan lokaci abu ne da ba za a guje masa ba bayan cire tallafin.
Shugaban ƙaramar hukumar da ya koma sana'ar ɗinki a Kano
Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Kano, Abdullahi Ghali (Basaf) ya ce ci gaba da sana'ar ɗinki tamkar yin rayuwarsa ce ta yau da kullum.
Comrade Basaf, ya ce ya koma sana'ar ɗinkin ne don nuna wa jama'a cewa siyasa bai kamata ta zama hanyar rayuwa ta dindindin ba.
Bidiyo - Abba Auwalu/Zahraddeen Lawan
An yi garkuwa da ɗan Jamus a Jamhuriyar Nijar
Rahotanni sun ce wasu mayaƙan da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar Islamic State in the Greater Sahara (ISGS) sun yi garkuwa da wani ɗan ƙasar Jamus wanda ɗan asalin asalin Turkiyya ne a yankin Tahoua da ke tsakiyar Jamhuriyar Nijar.
Lamarin ya sake nuna cewa ƙungiyar na ci gaba da kasancewa a yankin, kamar yadda shafin Points Chauds mai zaman kansa ya ruwaito a ranar 30 ga Yuli.
Rahoton ya ce mutumin ya isa birnin Niamey ne daga Algiers, kafin ya tafi yankin Tahoua domin harkokin kasuwancin zinariya. A hanyarsa ne ake zargin mayaƙan ISGS suka tare shi suka yi garkuwa da shi.
Rahoton ya ƙara da cewa: "Daga baya, masu garkuwar sun tuntuɓi iyalansa domin tabbatar musu cewa suna tsare da shi."
Wannan garkuwa da mutumin ta faru ne duk da ci gaba da hare-haren soji da gwamnatin Nijar tare da ƙawayenta na ƙawancen ƙasashen Sahel (AES) ke yi domin ƙwato yankunan da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi suka mamaye.
Sai dai har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da tsananta a sassa da dama na ƙasar, musamman yankunan kan iyaka, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin sauƙi.
Yankin Tahoua, wanda ke da muhimmanci ta fuskar kasuwanci da haƙar ma'adinai, ya zama ɗaya daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta fi ƙamari a Nijar.
Ghana ta amince da ƙudurin mayar da mulkin ƙasar shekara biyar
Gwamnatin Ghana ta amince da wasu muhimman gyare-gyare da kwamitin yi wa kundin mulkin ƙasar garambawul ya gabatar, ciki har da tsawaita wa'adin mulkin shugaban ƙasa da na 'yan majalisa daga shekara huɗu zuwa shekara biyar, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na cikin ƙasar suka ruwaito a ranar 30 ga Yuli.
Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Dominic Aniye, ya ce: "Muna tunanin waɗannan zauye-zauyen za su yi. A ƙarƙashin tsarin wa'adin shekara huɗu na yanzu, watannin farko na kowane zangon mulki suna wucewa ne wajen karɓar mulki, sannan shekarar ƙarshe ta shige cikin shirye-shiryen zaɓe."
Ya ƙara da cewa: "Wa'adin shekara biyar zai ba kowace gwamnati isasshen lokaci wajen tsara manufofi, aiwatar da su da kuma tantance sakamakonsu."
Kwamitin ya miƙa rahotonsa na ƙarshe ga Shugaba John Mahama, inda ya ba da shawarar a yi wa kundin tsarin mulkin shekarar 1992 kwaskwarima.
Gwamnatin ta kuma amince da wasu shawarwari da suka haɗa da:
Ƙara yawan kujerun majalisa daga 276 zuwa 300.
Rage mafi ƙarancin shekarun da ake buƙata domin tsayawa takarar shugaban ƙasa daga 40 zuwa 35.
Sauran shawarwarin sun haɗa da:
Soke hukuncin kisa.
Taƙaita yawan ministoci zuwa 60 kacal.
Soke cikakken keɓewar shugaban ƙasa daga biyan haraji.
Taƙaita adadin alƙalan Kotun Ƙoli zuwa 19.
Samar da wa'adi guda ɗaya na shekara 10 ga Babban Alƙalin Ƙasa ba tare da damar sake naɗa shi ba.
Ana sa ran za a gabatar da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin nan da watan Oktoba, yayin da ake sa ran gudanar da ƙuri'ar raba gardama kan sauye-sauyen a shekarar 2027.
'Waɗanda suka sace ɗaliban Oyo sun buƙaci musaya da manyansu muka ƙi'
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce gwamnati ta ƙi amincewa da buƙatun masu garkuwa da mutanen da suka kai hari makarantu uku a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar a ranar 15 ga Mayu.
Maimakon haka, gwamnati ta mayar da hankali kan aikin ceto ɗaliban ne ta hanyar amfani da bayanan sirri, kamar yadda shafin jaridar Punch ya ruwaito a ranar 31 ga Yuli.
Tinubu ya bayyana haka ne a karon farko tun bayan da aka ceto aƙalla ɗalibai da malamai 39 a ranar 10 ga Yuli, yayin wata ganawa da tawagar sarakunan gargajiya daga jihar Oyo a Abuja.
Ya ce: "Mun ƙi tattaunawa kan biyan kuɗin fansa. Waɗannan masu aikata laifin sun buƙaci mu saki wasu daga cikin 'yan ƙungiyoyinsu da aka riga aka kama. Wannan na daga cikin sharuɗɗansu, baya ga kuɗin da suke nema."
Ya ƙara da cewa: "Mun ce babu wata yarjejeniya. Ba za mu tattauna da masu aikata laifi ba. Sun aikata kisan kai, kuma mun shirya murƙushe su. Suna da iyalai da kuma al'ummomin da suka fito."
Har ila yau, Tinubu ya danganta ƙaruwar sace-sacen mutane da hare-haren masu tayar da ƙayar baya a Najeriya da matsalolin tsaro da ke ƙasashen yankin Sahel.
Mawaƙiyar Afirka ta Kudu Tyla ta fasa zuwa Najeriya taron kalankuwa
Mawaƙiyar Afirka ta Kudu, Tyla, ta cire Najeriya a cikin jerin ƙasashen da za ta je domin taron kalankuwa da ta shirya gudanarwa a ƙasashen duniya da dama.
Ta shirya zuwa ƙasashen ne domin baje-kolin waƙoƙin sabon kundin waƙokinta.
Sai dai alamu sun nuna ta fasa zuwa Najeriya bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan nuna wariyar baƙi a ƙasarta ta Afirka ta Kudu.
A ranar Litinin ne Tyla ta sanar da ranakun rangadin , kuma a ciki ranaku uku na wasanni a nahiyar Afirka.
Da farko dai an tsara za ta raƙashe ne a a Legas ranar 22 ga Disamba ne.
Dubban baƙin-haure sun tsallaka Spain ta Morocco
Dubban ƙarin baƙin haure sun taru a kan bakin iyakar Ceuta, yankin Sifaniya da ke Arewacin Afirka, bayan da yankin ya fuskanci gagarumar kwararar masu shiga ƙasar a jiya Alhamis, karo na farko cikin shekara biyar.
Gwamnatin Sifaniya ta tura karin sojoji domin taimakawa wajen shawo kan lamarin, yayin da ake sa ran Firaminista Pedro Sánchez zai kai ziyara yankin na Ceuta a yau Juma'a.
Rahotanni sun ce hukumomin Maroko sun fara ɗaukar tsauraran matakai kan bakin hauren, inda a daren da ya gabata suka rika fesa wa bakin ruwa domin tarwatsa su.
Sifaniya ta ce ta cimma yarjejeniya da Maroko domin mayar da bakin hauren zuwa ƙasarsu cikin gaggawa.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin Maroko a kan batun. Jami'ai a Ceuta sun ce aƙalla mutum 15 sun mutu bayan da suka nutse a teku yayin da suke ƙoƙarin isa yankin na Sifaniya.
Kotu ta ba ƴansandan Brazil izinin binciken ɗan shugaban ƙasar
Wani alƙalin Kotun Koli ta Brazil ya bayar da izini ga ƴansanda su gudanar da binciken kan Fabio Lula da Silva, babban ɗan Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva, bayan an danganta shi da wata badaƙalar zamba da ta shafi maƙudan kuɗaɗe.
Ana zargin Fabio, wanda aka fi sani da Lulinha, da taimaka wa wani mai rajin neman tasiri a harkokin gwamnati da ke zaman kurkuku a yanzu, a mu'amalolinsa da Ma'aikatar Lafiya ta Brazil dangane da kasuwancin tabar wiwi da ake amfani da ita wajen magani.
Mutumin da ake magana a kansa an same shi da laifin damfarar ƴan fansho a wata shari'a ta daban a bara, kuma tuni an taɓa binciken Lulinha dangane da wannan batu.
Lauyoyin Fabio Lula da Silva sun shaida wa kafafen yaɗa labarai na Brazil cewa ba za su iya yin tsokaci kan sabon binciken ba, domin har yanzu ba su ga cikakkun bayanansa ba.
Shugaba Lula ya sha alwashin cewa ba za a nuna sani ko sabo ba a kan dan nasa.
Hamas ta amince ta ajiye makami a Gaza bayan tattaunawa da Trump
Bayan tattaunawar wata da watanni, ƙungiyar Hamas ta ce ta amince da wani shiri da Hukumar Zaman Lafiya ta Shugaban Amurka Donald Trump ta gabatar, na ta kwance damarar yaki gaba daya - ta ajiye makamanta a Zirin Gaza.
Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban abin tarihi, yana mai cewa ta zama wani muhimmin mataki na samar da sabuwar gwamnatin Falasɗinawa a Gaza.
Wakilin BBC a Gaza, wanda ke birnin Alkahira na Masar, ya ce shirin ya tanadi ƙididdige da adana manyan makaman Hamas da suka rage ƙarƙashin kulawar hukumomin Falasɗinawa.
Wakiliyar BBC ta ce, zuwa yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba.
Shugaba Trump dai ya ce dakarun Isra'ila za su fice daga Gaza da zarar an kammala kwance damarar Hamas da sauran ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai.
Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa, barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'atu babbar rana.
Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.
Facts Only
* Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, and Abdullahi Bello discussed the concept of Auren Mutu'a in Northern Nigeria.
* The Minister of Finance stated that funds from cutting fuel subsidies and reforming foreign aid are used for government payments and operational costs.
* Changes in the economy led to questions regarding the use of funds after subsidy removal.
* Before subsidy removal, foreign aid and fuel subsidy funds accounted for about five-tenths of national income.
* After reforms, revenue from oil sectors increased from 8% to 24%.
* Government employee salaries increased by almost twice, with the government setting a minimum salary to N70,000.
* The government increased spending on education and provided over N1.5 trillion in living allowance.
* The IMF did not support the view that the purchasing power of Nigerians would recover automatically.
* A former Kano State government official stated he continued his trade as a way to show that politics should not dictate daily life.
* Reports indicated an ISGS member was involved in an incident with a man from Algiers, who was allegedly involved in gold trade in Tahoua.
* Ghana reviewed its constitution and recommended changes including a four-year term for the president and reductions in ministerial numbers.
Executive Summary
Full Take
The narrative presents a complex interplay between macroeconomic policy shifts, security dynamics, and governance structures, suggesting that abstract economic adjustments have immediate, tangible social consequences. The discrepancy between official claims regarding revenue growth post-reform and the lived experience of the populace highlights a critical gap in information flow—where centralized figures about national wealth are presented alongside localized struggles over basic necessities. The story concerning subsidy removal and foreign aid exemplifies how top-down policy changes impact human agency; while macroeconomic indicators might show nominal growth, the actual distribution of resources is what shapes public perception and stability.
The juxtaposition of these economic concerns with reports on security incidents in the Sahel and constitutional reviews elsewhere reveals a thematic pattern: instability across various domains—economic control, security governance, and political legitimacy—is occurring simultaneously. The tension between state-level narratives (like those from the Ministry of Finance or Ghana's constitutional review) and ground realities (like local security concerns or the impact on daily living costs) suggests that cognitive sovereignty is challenged when official data does not align with lived experience. This demands an analysis of which metrics are prioritized in public discourse and who controls the framing of perceived success or failure.
The ambiguity regarding accountability—specifically concerning resource allocation following policy shifts, and the reported security situations juxtaposed with international diplomacy—creates a space where different realities coexist without immediate reconciliation. The system appears structured to manage visible outcomes while potentially obscuring the underlying structural shifts that create enduring disparities in well-being. What are the unstated assumptions driving the prioritization of certain statistics over others? And how does acknowledging this divergence inform the process of building resilient, locally-grounded decision-making?
Sentinel — Human
LIKELY_HUMAN (confidence: 0.2)
