Wasu yanbindiga sun kai hari a wasu kauyuka na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya inda suka kwashi mutane da ba a san yawan su ba a lokacin da suke Sallar Juma'a.
Yanbindigar sun kai hare-haren ne a ƙauyukan Dekara da Gidan Zana da Sabon Gida da Masaka da ke ƙaramar hukumar Borgu, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
Danmajalisar tarayya da ke wakiltar yankin, Hon Jafar Muhammad Shetiman Borgu ya tabbatar wa da BBC da harin inda ya ce har yanzu ba su iya tantance yawan mutanen da aka kwasa aka shiga daji da su ba.
Ya ce akwai wasu masallata da dama da aka yi wa yankan rago, yana mai cewa suna cikin tashin hankali.
"Wasu sun samu sun kuɓuto kuma akwai raunika na sara a jikinsu," in ji shi.
Ya ce ƴanbindigar sun shiga garin Dekara bayan kammala sallar Juma'a suka tattara mutane suka shiga daji da su.
"Yanbindigar sun yi wa Masallacin ƙawanya suka kwashi mutane suka tafi da su,"
Ya ƙara da cewa ƴanbindigar sun shiga wasu ƙauyuka makwabta suka sake ɗibar wasu mutanen bayan sallame Sallar Juma'a.
Ɗanmajalisar ya ce akwai matasa da dama cikin waɗanda aka ɗauka da kuma magidanta.
Dajin Borgu ya zama maɓuyar Lakurawa da Mamudawa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hare-haren a masallatan Juma'a ya ƙara haifar da damuwa kan girman matsalar yanayin tsaro a yankin Borgu, inda mutanen ƙauyukan yankin ke ci gaba da fuskantar hare-haren ƴanbindiga masu satar mutane.
Hon Jafar Muhammad Shetiman Borgu ya ce yankin da ke makwabtaka da jihar Kebbi da jihar Kwara da kuma Jamhuriyyar Benin ya kasance mafakar mayakan Lakurawa da Mamudawa.
Ya ce an samu saɓani tsakanin mayakan Lakurawa da Mamudawa bayan an shiga masallatan Juma'a an kwashi mutane an tafi daji da su.
"Wani ɓangare na ƴanbindigar ya nuna rashin amincewa da abin da aka yi na shiga masallatan Juma'a a kwashi mutane a shiga daji da su inda suka koma suna yaƙar juna," in ji shi.
Ɗanmajalisar ya ce suna tunanin sun deɓi matasa ne domin horar da su shiga ƙungiyarsu.
Amma ba za su iya tabbatar da ɓangaren mayaƙan da ya kwashi mutanen ba - Lakurawa ne ko Mamudawa.
A watanni da suka gabata wasu rahotanni sun tabbatar cewa mayakan da ake zargin na Lakurawa ne sun shiga wasu yankuna a Jihar Neja, inda suka tara mazauna gari suna masu wa'azi na nuna aƙidarsu tare da yi wa mutanen yankin barazana.
Mayaƙan sun yi hani da sata da haramta shan giya da zina tare da yin kira ga al'umma su bi umarnin shari'ar Musulunci.
Duk da jami'an tsaro na sanar da ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da ƴanbindiga amma ƙaruwar barazanar hare-hare a jihar Neja wani babban ƙalubale ne
Ko a makon da ya gabata an kashe mutum sama da 20 a yankin ƙaramar Hukumar Borgu.
A yankin ne ƴanbindiga suka saci ɗalibai sama da 200 a garin Papiri a watan Nuwamban 2025, kafin aka kuɓutar da su bayan shafe wata ɗaya hannun ƴanbindiga.
