Kofin Duniya na FIFA da za a ɗaga a New Jersey ranar Lahadi yana ɗauke da zinariya mai darajar kusan dala dubu 713,000 (£532,000) a cikin jikinsa mai nauyin kilogram 6.175, bisa wani bincike da London Stock Exchange Group (LSEG) ta gudanar.
Wani ɗan sassaƙa na Italiya mai suna Silvio Gazzaniga ne ya tsara shi, sannan aka ƙera shi a wurin aikin Bertoni da ke Milan. Ƙungiyar da za ta yi nasara a gasar za ta ɗaga kofin na ɗan lokaci ne kawai, sannan ta mayar da shi nan take.
Spain da Argentina za su fafata domin lashe kofin a ranar Lahadi bayan Spain ta doke Faransa da ci 2-0, yayin da Argentina ta doke Ingila da ci 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe.
Ƙasar da za ta yi nasara za ta koma gida da wani kwafin kofin da aka yi wa rufin zinariya, yayin da ainihin kofin zai koma rumbun adana kayayyaki na gidan tarihi da ke Zurich.
Daga Diego Maradona zuwa Zinedine Zidane, daga Ronaldo zuwa Bastian Schweinsteiger, manyan ƴan ƙwallon ƙafa sun rubuta sunayensu a tarihi ta hanyar ɗaga wannan kofin mai daraja.
Assasa sabon kofin
Tarihin kofin da ake amfani da shi a yanzu ya fara ne a shekarar 1974 bayan Brazil ta mallaki kofin Jules Rimet na dindindin.
A shekarar 1970, Brazil ta lashe gasar cin kofin duniya karo na uku a Mexico. Bisa dokar wancan lokacin, ƙasar da ta lashe gasar sau uku za ta riƙe kofin na dindindin. Hakan ya sa FIFA ta fara neman sabon kofi domin gasar shekarar 1974 da za a gudanar a Jamus ta Yamma.
An gabatar da zane-zane guda 53 daga masu fasaha daban-daban daga sassan duniya. Daga cikin waɗannan zane-zane, FIFA ta zaɓi aikin wani mashahurin mai sassaƙa na Italiya mai suna Silvio Gazzaniga.
Aikin Gazzaniga ya zama abin da duniya ke gani yanzu: hoton ƴan wasa biyu masu suna ɗaga duniya a sama, wanda ke nuna farin cikin nasara da haɗin kan duniya ta hanyar ƙwallon ƙafa.
Gazzaniga ya taɓa bayyana cewa: "Duniya tana da siffar ƙwallo, shi ya sa take kama da ƙwallon ƙafa."
Girma da darajarsa
Kofin Duniya na FIFA an yi shi ne da zinariya mai nauyin karat 18, wato zinariya mai tsarkin kashi 75 cikin 100.
Kofin yana da siffofi kamar haka:
- Tsawo: Santimita 36.8
- Nauyi: Kilogram 6.175
- Gindinsa: Santimita 13
Gindin kofin yana ɗauke da duwatsu masu daraja masu launin kore da ake kira malachite, waɗanda suke ƙara masa kyawun gani.
Duk da cewa zinariya ce ta fi ɗaukar hankali, darajar kofin ba ta tsaya ga kuɗin zinaren da aka yi shi da shi kawai ba. Tarihinsa, nasarorin da aka yi a ƙarƙashinsa, da kuma matsayin da yake da shi a zukatan magoya bayan ƙwallon ƙafa sun sa ya zama ɗaya daga cikin abubuwan wasanni mafi daraja a duniya.
Asalin kofin
An fara gabatar da kofin farko na gasar cin kofin duniya ne a shekarar 1930, lokacin da FIFA ta ƙaddamar da gasar farko a ƙarƙashin jagorancin Jules Rimet, wanda aka sanya wa kofin sunansa.
Rimet shi ne shugaban FIFA mafi dadewa a tarihi, inda ya riƙe shugabancin hukumar na tsawon shekara 33 daga 1921 zuwa 1954.
Wani mai sassaƙa ɗan Faransa mai suna Abel Lafleur ne ya ƙera kofin. Tsarinsa yana nuna Nike, wato baiwar nasara ta tsohuwar Girka, tana ɗaga wani kofi sama.
An ƙera kofin ne da azurfa mai rufin zinariya, sannan aka ɗora shi a kan dutse mai daraja mai suna lapis lazuli.
A lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, FIFA ta bayyana cewa wani jami'in ƙwallon ƙafa na Italiya mai suna Ottorino Barassi ya ɓoye kofin a cikin akwatin takalmi ƙarƙashin gadonsa a birnin Rome.
Ya yi hakan ne domin hana kofin faɗawa hannun sojojin Nazi.
Sau biyu ana sace kofin
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kimanin watanni kaɗan kafin fara gasar cin kofin duniya ta shekarar 1966 a Ingila, an sace kofin yayin da ake nuna shi a wani wajen baje-koli na jama'a.
Bayan bincike mai yawa, an gano kofin ta hanyar wani kare mai suna Pickles, inda ya gano kofin ne a nannaɗe a cikin jarida, ƙarƙashin wani shinge na lambu a kudancin birnin Landan.
Wannan lamari ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jan a game da tarihin kofin.
A shekarar 1970, Brazil ta zama ƙasa ta farko da ta lashe gasar cin kofin duniya sau uku.
A ƙarƙashin dokar FIFA ta lokacin, ƙasar da ta lashe kofin sau uku za ta mallaki kofin na dindindin.
Saboda haka, Brazil ta samu damar riƙe Kofin Jules Rimet har abada.
Sai dai a shekarar 1983, an sake sace kofin Jules Rimet, wannan karon daga hedikwatar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Brazil da ke birnin Rio de Janeiro.
Ba a sake gano kofin ba har yau.
Ana kyautata zaton an narkar da shi, kodayake ba a taɓa tabbatar da hakan ba a hukumance.
Ƙasashen da suka lashe gasar
Daga shekarar farko da aka fara gasar wato 1930 zuwa ta ƙarshe da aka fafata a Qatar a shekara 2022, ƙasashe takwas ne suka lashe gasar, inda Brazil ta lashe biyar, sai Jamus ke biye mata da huɗu:
- Brazil: 5
- Jamus: 4
- Italiya: 4
- Argentina: 3
- Faransa: 2
- Uruguay: 2
- Ingila: 1
- Spain: 1
Facts Only
* The FIFA World Cup trophy weighs 6.175 kilograms.
* It is made of gold, 75% gold.
* Sculptor Silvio Gazzaniga designed the trophy.
* It was cast at Bertoni in Milan.
* Spain and Argentina will compete for the trophy next.
* The trophy is kept in a storage facility in Zurich.
* Historical winners include Diego Maradona, Zinedine Zidane, Ronaldo, and Bastian Schweinsteiger.
* The current design features Malachite in the gold.
* It was first introduced in 1930 under Jules Rimet.
* Winners include Brazil (5), Japan (4), Italy (4), Argentina (3), France (2), Uruguay (2), England (1), and Spain (1).
Executive Summary
Full Take
Sentinel — Likely Human
The text reads like a human-written piece blending documented historical facts about the FIFA World Cup trophy with anecdotal history and opinion, rather than purely synthetic generation.
