- Marubuci, Masoud Azar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 9
Har yanzu ba a ganin Mojtaba Khamenei. Fiye da wata huɗu bayan maye gurbin mahaifin sa a matsayin sabon jagoran addinin Jamhuriyar Musulumci ta Iran, har yanzu ba a ga sabon jagoran ya bayyana ko dai a kafafen yaɗa labarai ko kuma a wajen taron jama'a ba.
An wallafa wasiƙun da aka alaƙanta da shi, amma babu wani labari a kan wajen da ya ke, babu wanda ya ji muryarsa, babu wanda ya ga hoton shi ko kuma rubutun da ya yi da hannunsa.
A yanzu kuma an fara alaƙanta rashin bayyanar ta shi da irin ta ɓuyar annabawa da kuma babban limamin Shi'a na 12.
Tsawon lokacin da aka ɗauka ba tare da bayyanar Mojtaba Khamenei ba ya janyo ana yaɗa raɗe-raɗi a kan shi. Donald Trump ya ce akwai yiyuwar ya riga ya rasu.
A cikin Iran kuma, shugaba Masoud Pezeshkian ne kaɗai ya fito ya sanar cewa ya gan shi ido da ido. Jami'an gwamnati sun ce sabon jagoran addinin na Iran ya ƙi bayyana ne saboda dalilai na tsaro.
Wani abu da ya ɗauki hankalin kafafen yaɗa labarai a ƴan kwanakin nan shi ne yunƙurin mutane irin su Mohammad Mehdi Mirbagheri, jagoran Paydari, na nuna cewa dama akwai rashin bayyanar Mojtaba Khamenei a cikin tsarin Shi'anci abin da wasu ke kira ɓuya ko Ghaiba.
Mohammad Mehdi Mirbagheri, ɗaya daga cikin manyan malaman Iran kuma ɗan kwamitin ƙwararru masu tsattsauran ra'ayin rashin sasanci da ƙasashen yamma, ya faɗa a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, game da ɓuyar Mojtaba Khamenei cewa hakan abu ne mai yiyuwa kamar yadda aka sani a tarihin rayuwar annabawa da kuma babban limamin Shi'a na 12 don haka ya ce "babu wata matsala da cewa Imam Mojtaba Khamenei ya ɓuya kamar yadda Limamin Shi'a ya yi a wancan lokacin.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan sanarwa ta fitattacen malamin inda ya alaƙanta ɓuyar Mojtaba Khamenei da wadda annabawa da babban limamin Shi'a suka yi ta sake dawo da muhawara kan aƙidar 'ɓuya' ko Ghaiba, ɗaya daga cikin manyan shika-shikan da Shi'a ta ginu a kai.
Wasu ƙissoshin Musulunci sun nuna cewa daga cikin annabawa 1,400 da aka aiko duniya, wasu sun ɓuya daga shiga al'umma ko dai na ɗan lokaci ko kuma na lokaci mai tsawo saboda ɗaukaka da baiwa.
Daga cikin annabawan da ƙissoshin Musulumci suka ce sun shiga ɓuya akwai Idrisa da Nuhu da Ibrahim da Shu'aib da Musa da Suleiman da kuma Isa.
Wannan ya janyo tambaya a kan matsayin ''ɓuya'' a tarihin Shi'a: Shin yarda ce kawai ta wasu mutane ko kuwa tana da alaƙa da siyasa da zamantakewar yau da kullum?
Ko akwai wasu misalanta a sauran ƙasashen Musulmai ko kuma wasu ƙungiyoyin siyasa? Sannan kuma wata tambayar mai muhimmanci kan ko wane tasiri shugabanci daga ɓuya zai yi ga gwamnati da al'ummar Iran ta yanzu?
Ghaiba ko Ɓuya a tarihin Shi'a
A cikin shekaru 47 da suka gabata, abubuwa da dama sun taso game da addini da siyasa, waɗanda aka alaƙanta su da aƙidar ''ɓuya.''
A farkon batun gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta ƙirƙiro wani tsari da aka ce zai ci gaba har zuwa bayyanar babban limamin Shi'a, wanda suka ce za a miƙa wa tutar Musulunci kuma zai zamo ''mai ceton duniya''.
Daga nan aka fara rera take irin su ''Allah, Allah kare Khomeini har zuwa bayyanar Mahdi,'' da kwatanta Sayyid Ali Khamenei da ''Sayyadi Khorasani,'' wanda aka ce makusanci ne na babban limamin Shi'a na 12 da kuma gabatar da shugabannin Jamhuriyar Musulunci a matsayin ''Mataimakan Imam na lokacin''.
Waɗannan kalaman kambamawa da farfaganda sun ci gaba da yaɗuwa a cikin shekaru kusan 50. A yanzu wasu magoya bayan Mojtaba Khamenei suna mashi kirari da irin waɗannan kalamai.
A labarin da aka bayar kan limamin Shi'a na 12, bayan rasuwar Imam Hassan al-Askari a shekarar 260 bayan hijira, ɗan shi Muhammad ibn Hassan, limamin Shi'a na 12 ya ɓuya inda aka daina ganin shi a cikin jama'a.
Mabiya Shi'a sun yarda cewa da farko ya riƙa magana da mabiyansa ta hannun wasu wakilai na musamman guda huɗu har na tsawon shekara 70 da ake ƙira ''ƙaramar ɓuya'' daga nan kuma sai ya shiga ''babbar ɓuya'' wadda har yanzu yake a ɓoye.
Malaman tarihin Musulunci da dama sun yarda cewa tasirin ɓuyar limamin Shi'ar bai tsaya kan addini kaɗai ba. Wasu na da yaƙinin cewa abin na da alaƙa da ƙalubalen shugabanci.
Bayan rasuwar limamin Shi'a na 11, mabiya aƙidar sun faɗa cikin tunanin yadda za a ci gaba da tsarin limancin. Saboda haka aka riƙe aƙidar Ghaiba domin ci gaba da jagorancin ƙasar da sunan limamin ba tare da kasancewarsa a zahiri ba.
A cewar masanin tarihin Musulunci ɗan ƙasarJamus, Wilfred Madelung, amfani da tsarin aƙidar Ghaiba ko ɓuya ''hanya ce ta kaucewa duk wani abu da zai kawar da al'adar mulkin limancin Shi'a'' kuma sannu a hankali sai ta zamo ƙashin bayan kambama tasirin limamin Shi'a na 12.
Samar da majalisar shura a lokacin ''ɓuya''
Duk da cewa waɗanda suka yarda da aƙidar ɓuyar limamin shi'a na 12 na tafiya da yardar cewa ba za a riƙa ganin jagoransu a bainar jama'a ba, hakan ba ya nufin ba janye addini baki ɗaya daga harkar jagoranci.
Tun daga ayyana ɓuyar jagoran, tambayar da mabiya Shi'a suka fuskanta ita ce, a lokacin da limamin baya nan wa zai riƙa yanke hukunci kan hukunce-hukuncen addini da kuma bayar da fatawa kan abubuwan da suka shafi al'umma.
A hankali amsar wannan tambaya ta share fagen samar da majalisar shura. Da farko aikinsu ya taƙaita ga zartar da hukunci da kula da harkokin addini, amma a hankali sai ƙarfin su ya ƙaru.
A hankali suka zama su ne mahukunta, su ne alƙalai kuma masu tafiyar da harkokin addini, har ma a wasu lokutan suna shiga harkar siyasa.
Wannan tsari ya shiga sabon zango a ƙarni na 20, inda juyin juya halin 1979 ya janyo sauye-sauye da dama.
Ruhollah Khomeini ya haƙiƙance cewa ƴan majalisar shura suna da ƙarfin kafa gwamnati a lokacin da aka shiga yanayi na ɓuyar jagoran addini.
Ya ce: ''ƴan majalisar shurar lokacinmu suna da ikon kafa gwamnati mai adalci.''
Dariush Mohammadpour, wani mai bincike kan addini kuma farfesa a cibiyar Ismaili ta London, ya shaida wa BBC cewa: "A farkon juyin juya halin jagoran addini shi ne mataimakin Imam amma a hankali sai ƙarfin ikonsa ya ƙaru..."
Domin ƙarin bayani kan iƙirarinsa, Mr. Mohammadpour ya ce "Misalai biyu da ke tabbatar da wannan su ne matsayarsa kan sallar Juma'a da kuma dakatar da zuwa aikin hajji na wucin gadi a zamanin Khomeini wanda ya ɗauki matakin saboda rashin fahimtar da ke tsakaninsa da gwamnatin Saudiyya, inda Khomeini ya ƙwace ɗaya daga cikin aikin majalisar shura.
Daga wannan matsaya, samun amincewa da gwamnatin Jamhuriyar Musuluncin na zuwa ne ba daga babban limamin da ya ɓuya ba, domin haka aƙidar ɓuyar limamin Shi'a da mabiya suna yarda da ita ba ta tsaya kan addini kaɗai ba, ta shiga har da siyasa.
Ta yaya ɓuyan Mojtaba Khamenei ta banbanta da ta Imam Mahdi?
Duk da ƙoƙarin da mutane irin su Mohammad Mehdi Mirbagheri suka yi na alaƙanta ɓuyar Mojtaba Khamenei da ta annabawa da babban limamin Shi'a na 12, masu nazari da dama sun yarda cewa akwai banbanci a tsakanin yanayin biyu.
Da farko dai, a aƙidar Shi'a, ɓuyar limami na 12 abu ne da Allah ya tsara. Ana yi wa limamin kallon wanda Allah ya zaɓa kuma ɓuyar tasa ba ta da nasaba da siyasa.
A gefe guda kuma suna nuna cewa jagoran addinin Iran yana da matsayi a siyasa wanda kundin mulkin ƙasa da majalisar dokoki suka ba shi.
Babu shakka akwai masu ganin cewa zaɓar Mojtaba Khamenei, abu ne da ƙaddara ta zo da su, kuma babban limamin Shi'a na da hannu a kasancewar wannan ƙaddara.
Banbanci na biyu shi ne aƙidar Shi'a cewa limaminsu ya ɓuya ne domin ci gaba da jaddada rayuwar shi, kuma suka fayyace lokacin sake bayyanar shi.
Dariush Mohammadpour, wani mai nazarin addini ya yi martani ga kalaman mutane irin Mohammad Mehdi Mirbagheri:
"Daga yanzu ba za a riƙa alaƙanta ɓuyar da addini ba ko aƙidar Shi'a ba, a madadin haka za a riƙa mata kallon wata hanya ta rarraba madafun iko na siyasa ga wasu mutane waɗanda ke da matsala da bayyanar jagoran.
Farfesan a cibiyar Ismaili ta London ya ce: "Shekara 30 da Ali Khamenei ya yi yana jagoranci kuma ana ganin shi a cikin jama'a ya zamo matsala hatta a tsakanin ƴan gani kasheninsa. Saboda haka jagoran da ke tafiyar da mulki a ɓoye, wanda ba a gani ko ji, dama ce ta kwantar da waccan ƙurar.''
Wane tasiri rashin bayyanar Mojtaba Khamenei ke yi ga al'ummar Iran?
Ana iya nazari kan tsawon lokacin da jagoran addinin Iran ya yi a ɓoye ta fuskoki biyu: tasirinsa kan addini da kuma tasirinsa ga siyasa da inganta jagoranci.
A addinance, al'ummar Iran ta banbanta da aƙidar Shi'a da aka sani a baya.
A shekarun baya-bayan nan abubuwan da suka taso na rashin gamsuwa da yadda wasu malaman addini ke tafiyar da harkoki da wayewar duniya kan aminci tsakanin mabiya addinai daban-daban ya sa an sauya daga yadda mutane suka saba riƙo da addini a baya.
Domin haka, ga al'ummar da ta shiga wannan hali, cusa mata aƙidar jagoranci a ɓoye abu ne da zai buɗe babin tattaunawa da muhawara tsakanin cibiyoyin addini da kuma mabiya.
Daga ɓangaren siyasa kuma, a bisa tsarin siyasar da ake yi yanzu ta zamani, bayyanar shugaba ana ganin shi a zahiri na da tasiri sosai domin abu ne mai tabbatar da ƙarfin iko.
Kasancewar shugaba a cikin mutanen da yake jagoranta musamman a lokacin rikici, da gabatar masu da jawabi da tattaunawa da su kai tsaye wata hanya ce ta kwatar da hankali da bayar da tabbacin jagoranci.
Cigaba da ɓoyon shugaba, duk da cewa tana iya zama mai amfani saboda tsaro, abu ne da zai iya samar da giɓi a tsakanin gwamnati da al'ummar da kuma ya buɗe kafar yaɗa jita-jita game da yadda ake tafiyar da gwamnati.
Masu goyon bayan gwamnati na iya jayayya cewa a zamanin da ake ciki na kafafen sadarwa na zamani, gudanar da mulki ba ya dogara kan bayyanar jagora a zahiri, inda suke ganin aikewa da saƙonni da umarni ya wadatar wajen ci gaba da mulkar al'umma.
Amma kasancewar jagorori a zahirance a lokacin rikici da tashin hankali wani abu ne da ke tabbatar da iko da kwantar da hankali.
Da yake jaddada cewa jagororin al'umma na sane da muhimmancin samun yardar jama'arsu, Dariush Mohammadpour ya ce: "Idan shugabanni suka jajirce wajen bin tsarin da ya yi aiki a baya wajen tafiyar da harkokin mulki to ba za su yi rashin nasara ba.''
Da ya ke amsa tambayar ko kalaman malamai irin su Mr. Mirbagheri na iya tasiri kan mabiya, sai Mr. Mohammadpour ya ce: "Nazarin da na yi ya nuna cewa abu ne mai wahala.
Jamhuriyar Musulumci ta samu shekaru 50 a ƙarkashin jagorancin shura kuma da shugabanni jarumai biyu, Khomeini da Khamenei, ɗaya mai kwarjini da ƙarfin iko ɗaya kuma ƙwararre a jagorancin siyasa da soja, kuma duk a zamaninsu an fuskanci manyan ƙalubalai, amma duk da haka sun tafiyar da shura lafiya lau.
Ta yaya muke zaton wani da ya fi su karsashi da zafin nama zai iya tafiyar da harkoki ta hanyar da mafi yawan al'umma suka dawo daga rakiyarta? Irin wannan tunanin zai fuskanci turjiya sosai tsakanin majalisar shura da malamai.
Ko ma dai ya ta kaya, rashin bayyanar Khamenei na wucin gadi ne, ƙila a iya bayyana ta matsayin matakin tsaro saboda halin da ake ciki.
Amma idan aka ci gaba a haka, ko aka nemai ta zama ɓuya ta dindindin, Jamhuriyar Musulumci ta Iran za ta fuskanci gagarumar matsala irin wadda Taliban ta yi fama da ita wajen ɓoye mutuwar Mullah Omar, lamarin da ya janyo durƙushewar ƙungiyar.
Da farko dai, ci gaba da ɓoye shi zai iya janyo jita-jita a kan mutuwar Mojtaba Khamenei da kuma sanya jama'a su fara tunanin ko an kashe shi a ranar farko ta yaƙin, ko kuma ya rasu bayan samun rauni daga harin Isra'ila da Amurka.
A gefe guda kuma da alama jagororin Iran ba za su iya ci gaba da kawar da tunanin abubuwa da dama game da rashin bayyanar Mojtaba Khamenei a zukatan mabiya ba, abin da kawai ake iya cewa shi ne tunanin ya ɓuyo domin tabbatar da tsaron shi.
Facts Only
Mojtaba Khamenei has not appeared publicly.
No statements have been heard from him on social media or in public gatherings.
Official government statements cited security reasons for his non-disclosure.
Mohammad Mehdi Mirbagheri suggested the absence of Mojtaba Khamenei might be related to *buyar* or *Ghaiba*.
The lineage of the 12th Shia Imam is linked to Muhammad ibn Hassan, the son of Hassan al-Askari.
Scholars have noted that the concealment of leadership has been linked to political concerns.
Some Shia scholars suggest the doctrine of *Ghaiba* applies to the Imams and their occultation.
Executive Summary
Full Take
Sentinel — Human
This text functions as a detailed, opinion-based analysis drawing connections between religious doctrines (Shi'a belief in Ghaiba) and the political status of the Iranian leadership, supported by cited scholarly perspectives.
