Iran ta ce ta harbo jirgin yaƙin Amurka mara matuƙi a mashigar Hormuz
Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce ta harbo wani jirgin yaƙin Amurka mara matuƙi kirar MQ-9 a sararin mashigar Hormuz.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce ta harbo jirgin ne da wani sabon makami da rundunar ta ƙera.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana ranar ko lokacin da aka harbo jirgin ba.
Har zuwa yanzu, rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ba ta tabbatar ko musanta rahoton ba.
'Yanbindiga sun kashe mutum 18 ciki harda sojoji huɗu a Zamfara da Sokoto
Aƙalla mutum 18, ciki har da sojoji huɗu ne suka mutu bayan wasu 'yanbindiga sun kai hare-hare a wasu al'ummomi da ke jihohin Zamfara da Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya.
A jihar Zamfara, mazauna Kasuwar Daji sun ce maharan sun mamaye wani sansanin sojoji kafin su yi garkuwa da fiye da mutum 100 daga ƙauyen.
Rahotanni sun ce daga baya maharan sun saki matan da suka kama, amma har yanzu suna riƙe da kusan maza 52.
A jihar Sakkwato kuwa, an ce 'yanbindigar sun shafe sa'o'i suna kai hare-hare gida-gida a ƙauyen Lajinge da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, inda suka kashe fararen hula, suka sace dabbobi tare da ƙone wani gida.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai wani magidanci da 'ya'yansa maza biyu da aka ce sun ƙone da ransu yayin da suke ɓoye a cikin gida.
Shaidu sun kuma ce an yi garkuwa da wasu mata biyu, yayin da har yanzu hukumomi ba su fitar da bayaninsu kan hare-haren ba.
Majalisar masana ta Iran ta yi gargaɗi kan yarda da Amurka
Majalisar Masana ta Iran ta yi gargaɗi game da amincewa da Amurka, tana mai cewa abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna cewa dogaro da Washington ko fatan cimma yarjejeniya da ita ba zai haifar da sakamako mai kyau ba.
A cikin wata sanarwa, majalisar ta ce karya alkawuran da Amurka ta yi ya nuna cewa amincewa da ita "mafarki ne marar tushe"
Majalisar ta kuma ce duk wani kira na sassautawa ko mika wuya da sunan kare zaman lafiya cin amana ne da bai kamata a amince da shi ba.
Ta jaddada cewa duk wani mataki da Iran za ta ɗauka dole ne ya kasance daidai da umarni da jagorancin Jagoran Ƙolin ƙasar, Mojtaba Khamenei.
An saki alƙalin babbar kotun Kebbi da aka sace
An saki alƙalin babbar kotun jihar Kebbi, Justice Faruku Bunza, wanda aka yi garkuwa da shi mako guda da ya wuce a ƙaramar hukumar Bunza.
A cikin wata sanarwar da rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta fitar, mai magana da yawunta Bashir Usman ya ce an tabbatar da sakin alkalin a ranar Litinin, inda iyalansa da ma’aikatar shari’a ta jihar suka tabbatar da komawarsa gida cikin ƙoshin lafiya.
Rundunar ta ce duk da cewa masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa, ba a biya su ko sisi ba kafin sakin alkalin.
Ta kuma bayyana cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano tare da kama mutanen da ke da hannu a sace alkalin domin su fuskanci hukunci a gaban doka.
Jami’in soja da ɗansanda sun mutu yayin daƙile harin ’yanbindiga a zamfara
Rundunar sojin Najeriya ta ce wani jami’inta da ɗansanda sun rasa rayukansu yayin da suke daƙile wani hari da ’yanbindiga suka kai sansanin sojoji da ke Kasuwan Daji a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara.
Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce maharan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin da misalin ƙarfe 1:40 na safiyar ranar 2 ga Agusta, amma dakarun da ke wurin sun gano yunƙurin da wuri tare da mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa.
Bayan artabun, ƙarin dakaru sun bi sahun maharan, inda suka samu nasarar kuɓutar da mutum tara daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin harin.
Rundunar ta kuma ce sojoji biyu sun jikkata sakamakon harbin bindiga kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
Rundunar ta kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa jami’an tsaro shida ne suka mutu, tana mai jaddada cewa jami’in soja ɗaya da ɗansanda ɗaya ne suka rasa rayukansu.
Iran ta ce ba ta wata tattaunawa da Amurka a halin yanzu
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce a halin yanzu babu wata tattaunawa da ke gudana tsakanin Iran da Amurka, duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa za a fara sabbin tattaunawa a yau Litinin.
Baghaei ya bayyana cewa a yanzu Tehran ta fi mayar da hankali kan tattaunawar da take yi da Oman game da mashigar Hormuz, wadda ta shafe kwanaki takwas tana gudana.
Ya ce duk wata fahimta da ake samu da Oman ba tana nufin an buɗe mashigin Hormuz ba har sai an tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.
Baghaei ya kuma jaddada cewa rufe mashigin Hormuz ya biyo bayan hare-haren Amurka da Isra'ila ne, ba saboda saɓani tsakanin Iran da Oman ba.
A cewarsa, Iran da Oman na tattaunawa kan wata sabuwar hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa.
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wasu da take zargi da yi wa Isra'ila leƙen asiri
Hukumar shari’ar Iran ta sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan Omid Behzad da Pouria Safvat a safiyar Litinin, bayan kotu ta same su da laifin yi wa Isra’ila leƙen asiri.
A cewar kamfanin yaɗa labaran ma’aikatar shari’ar Iran, Mizan, mutanen biyu sun kasance suna tattarawa tare da aika wa hukumar leƙen asirin Isra’ila ta Mossad bayanai, hotuna da kuma bayanan wuraren da cibiyoyin soji da na tsaro na Iran suke.
Mahukuntan Iran sun ce irin waɗannan bayanai sun taimaka wajen gudanar da ayyukan leƙen asiri da suka shafi tsaron ƙasar.
Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da wasu lauyoyi sun dade suna nuna damuwa kan yadda ake gudanar da irin waɗannan shari’o’i a Iran, suna zargin cewa ana gaggauta aiwatar da hukuncin kisa ba tare da tabbatar da cikakken tsarin shari’a mai adalci ba.
Sun kuma ce rashin bai wa waɗanda ake tuhuma damar samun lauya yadda ya kamata na daga cikin matsalolin da ke haifar da tambayoyi kan adalcin irin waɗannan hukunci.
Iran na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya da Pakistan kafin tattaunawarta da Amurka
Iran na ci gaba da ƙarfafa hulɗarta da Saudiyya da Pakistan ta hanyar tattaunawa da manyan jami'an ƙasashen biyu, a daidai lokacin da ake sa ran fara sabon zagayen tattaunawa tsakanin Tehran da Washington cikin sa'o'i masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran (IRNA) ya ruwaito cewa ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araqchi, ya yi tattaunawa ta biyu a ranar Lahadi da takwaransa na Saudiyya, Faisal bin Farhan Al Saud.
Haka kuma ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Pakistan, sannan daga bisani ya tuntubi shugaban rundunar sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, wanda ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu tasiri a harkokin tsaro da siyasar ƙasar.
Wadannan tattaunawa na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa za a fara sabon zagayen tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, inda za a mayar da hankali kan batutuwan mashigin ruwa na Hormuz da kuma shirin nukiliyar Iran.
Trump ya sanar da fara sabbin tattaunawa da Iran a yau Litinin
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa za a fara sabbin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a yau Litinin, bayan sanarwar da ya yi a daren jiya game da janye wasu hare-haren da aka shirya kai wa Iran.
Trump ya ce a halin yanzu akwai fahimta kan batun mashigar Hormuz, kuma yana da yakinin cewa za a cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran.
Trump ta fadi hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One a ranar Lahadi.
A gefe guda kuma, ministocin harkokin wajen Iran, Saudiyya, Pakistan, Qatar da Jordan na ci gaba da gudanar da tattaunawa da shawarwari, waɗanda ake ganin sun fi mayar da hankali kan tattaunawar da ke tsakanin Tehran da Washington.
Assalamu alaikum
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.
Facts Only
* The IRGC claims to have captured an MQ-9 warplane and a missile over the Hormuz Strait.
* The statement did not specify the date or time of the capture.
* CENTCOM has not confirmed the reports regarding the aircraft.
* At least eighteen people, including four soldiers, died in raids in Zamfara and Sokoto.
* In Zamfara, victims allegedly killed over 100 civilians before confrontation.
* In Sokoto, victims reportedly killed livestock and seized property during raids.
* Some of those killed were allegedly women; some men were reportedly paraded while hiding in homes.
* Two men were reportedly paraded with their ransoms while hiding.
* Alqin was released from Bunza prison on a Sunday, confirmed by his family and legal staff.
* The Nigerian military lost a soldier and one prisoner during an operation in Zamfara.
* Operation FANSAN YAMMA resulted in the capture of some individuals, with two soldiers and one prisoner killed.
Executive Summary
Full Take
The narrative presents several distinct threads: maritime/geopolitical tension, internal security violence, and a significant challenge to external alignment. The juxtaposition of an IRGC claim regarding an aircraft over Hormuz—a critical choke point—with reports of internal mass killings in Nigeria highlights the fragmented nature of conflict reporting where specialized military actions are mixed with localized atrocity documentation.
The Iranian Majalis-e-Shura's explicit rejection of dependency on the United States, framing trust in Washington as "unfounded fantasy," signals a strategic pivot toward asserting sovereign decision-making against external influence. This reflection is amplified by the focus on bilateral discussions, specifically with Oman regarding the Hormuz Strait, suggesting that immediate security concerns are being prioritized over established geopolitical alignments.
The pattern of internal violence—where killings result in the seizure of property and the alleged fate of detainees—suggests a nexus where security operations bleed into broader governance, raising questions about accountability mechanisms within the operational theaters cited by sources. Furthermore, the documented efforts to secure prisoner releases and the subsequent investigation reflect a struggle to enforce legal structures amidst conflict, revealing the tension between kinetic action and due process. This dynamic suggests that sovereignty is being contested not just on the international stage, but also within domestic security frameworks where transparency and adherence to justice remain elusive benchmarks for trust.
Bridge Questions: How do the stated goals of asserting sovereign decision-making reconcile with the operational realities described in the reports of internal violence? What mechanisms are necessary to ensure that accountability for security actions, both internal and external, aligns with principles of justice? What are the long-term consequences when geopolitical discussions focus on immediate control (like the Strait) while underlying domestic stability remains fractured?
Sentinel — Human
The text exhibits characteristics of compiled journalistic reporting, weaving together geopolitical news and localized incident reports, suggesting human editorial structuring rather than pure synthetic generation.
